Connect with us

Featured

Ganduje Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Sa’o’i Kadan Bayan Zuwan Su Atiku da El-Rufai 

Shugaban Jam’iyyar (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, zuwa gidan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna a ranar Juma’a 11 ga Afrilu, 2025.

Wannan ziyara ta zo ne awanni kadan bayan da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyun adawa a Najeriya suka kai wa shugaba Buhari ziyara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya jagoranci wasu fitattun ‘yan siyasa ciki har da Nasir El-Rufa’i da Aminu Waziri Tambuwal zuwa wurin Buhari a Kaduna.

Wasu masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa, wannan ziyara wani yunkuri ne na haɗa kai tsakanin jam’iyyun adawa domin kalubalantar jamiyyar APC a zaɓe mai zuwa na 2027.

Duk da babu wata masaniya game da dalilin ziyarar kwamitin gudanarwar na APC, sai dai akwai zargin yiwuwar ficewar ɓangaren tsohuwar jamiyyar CPC daga jam’iyyar APC, biyo bayan sauya sheƙar da wasu mambobin jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Sai da tun farkon watan da ya gabata, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet