Featured
Wani Abun Fashewa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Fasinjoji 9 A Borno
Wani bom da ya fashe ya yi sanadin mutuwar fasinjoji tara da ke tafiya a kan titin Maiduguri-Damboa a Jihar Borno.
Jaridar The Punch ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana a ranar Asabar 12 ga Afrilu, 2025.
Direbobin da suka bi hanyar bayan faruwar lamarin sun tabbatar da cewa abin ya jawo cunkoso, inda mutane suka taru domin nuna alhini kafin daga bisani jami’an tsaro su kwashe gawarwakin.
Wani direban da ya roƙi a ɓoye sunansa ya ce, “Da wuya a fahimci abin da ya haddasa hadarin. Amma abin da muke da tabbaci a kai shi ne ba hatsari ne tsakanin motoci ba. Idan ka ga yadda motar ta lalace, za ka gane cewa fashewa ce ta auku saboda ta kone sosai har ba a iya ganewa.”
“Abin da aka ce mana shi ne motar ta taka wani abu mai fashewa da ke kusa da gefen hanya, inda gaba ɗaya fasinjoji tara suka mutu nan take.”
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, don jin cikakken bayani, ya roƙi a ba shi lokaci domin tattara bayanan da suka dace kafin ya fitar da sanarwa ga jama’a.
