Connect with us

Featured

Kano: An Dakatar Da Ma’aikatan Shari’a Tare Da Gargadin Wasu Manayan Alƙalai

Hukumar kula da ma’aikatan Kotuna ta jihar Kano, ta ɗauki matakin dakatar da wasu Rijistaran kotu guda biyu da dakatar da albashin su na tsawon watanni shida shida, tare da bayar da takardar gargaɗi da jan kunne ga wasu manyan Alƙalan kotunan Shari’ar Muslunci guda biyu a jihar.

Mai magana da yawun babbar kotun Kano Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan, ta cikin sanarwar da ya aikewa manema labarai, ya ce ɗaukar wannan matakin ya biyo bayan taron hukumar karo na 80, da aka gudanar a ranar 22 ga watan Afrilun 2025, cikin shirinta na dawo da daraja da kimar da ɓangaren yake da shi a idanun al’umma a Duniya.

A cewar Baba Jibo, ma’aikatan da aka dakatar sun haɗar da Ibrahim Adamu, mai matsayin Principal Rijistere, tare da dakatar da albashin sa tsawon watanni shida, da kuma jinkirta ƙara masa matsayi, sakamakon samun sa da laifin kalaman ɓatanci da cin zarafi, da kuma gwada ƙarfi akan shugabansa a wajen aiki,

Ya ce yin hakan ya kasance laifi, tare da saɓawa da dokokin aikin na kundin tsarin tafiyar da aiki na jihar Kano, da kuma ƙa’idojin aikin Kotu.

Ya ci gaba da cewa, “Hukumar ta ce ganin cewar wannan shi ne karo na biyu da Ibrahim ya yi irin wannan laifi, kuma an bashi takardar gargaɗi tare da bayyana a gaban kwamitin ladaftarwa, a don haka ne aka ɗauki wannan mataki akan sa don aiwatar da takunkumin Shari’a a kansa, “in ji Baba Jibo”.

Haka kuma, akwai wani mai suna Mai Gida Lawan, mai matsayin Principal Rijistere, daga sashin kotun ɗaukaka ƙara ta shari’ar Muslunci, wanda kwamitin hukumar ladaftarwar ya same shi da laifin karbar cin hanci ta hanyar yin ƙarya, inda aka ɗauki matakin rage masa albashi daga na 13 zuwa 12, da dakatar da shi na tsawon watanni shida ba tare da bashi albashi ba.

Baba Jibo, ya kuma ce, an ɗauki matakin miƙa takardar gargaɗi ga babban alƙalin kotun shari’ar Muslunci Alƙali Ibrahim Mansur, bisa samun hujjojin da suka tabbatar da cewar ya yi kalamai marasa daɗi ga wani sa ke da shari’a a gaban sa.

Har ila yau, hukumar da ke kula da ma’aikatan Kotu ta jihar Kano, Judiciary Service Commission, ta miƙawa babba alƙalin babbar kotun shari’ar Muslunci Nasiru Ahmad, bisa samun sa da laifin yin umarni, da garƙame wani a ɗakin ajiye waɗanda ake zargi da laifi, na ƙashin kan sa ba tare da yin amfani da Shari’a ba.

“Hukumar mu ta nanata cewar dole ne kowanne alƙali ya yi amfani da iya ikon da dokoki suka bashi, cikin gaskiya da riƙon amana, don kiyaye wa tare da samun ƙwarin gwiwa a ɓangaren Shari’a, a ƙokarin hukumar na yaƙi da rashin gaskiya, “in ji Jibo”.

Hukumar ta kuma bukaci dukkanin ma’aikatan Shari’a da ma’aikatan Kotu, tare da tunatar da su cewar, su gudanar da aikin su ta hanyar nuna Ɗa’a da kuma girmamawa, kamar yadda jama’ar Kano suka ba su amana, kamar yadda tashar Dala FM Kano, ta ruwaito.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet