Featured
Nijeriya Ta Yi Wani Gargadi Kan Barazanar Damfara Da Bautarwa Ta Intanet
Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta bai wa ‘yan ƙasarta shawarar tantance duk wani tayin aiki ta hanyar hukumomin gwamnati kafin su karɓa domin zuwa ƙasashen waje.
Nijeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar kan barazanar bautar da mutane tamkar bayi a ƙasashen ƙetare ta amfani da shafukan intanet.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X wadda mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya sanya wa hannu, ta ce ana yaudarar ‘yan Nijeriya musamman matasa da alƙawarin aiki na ƙarya a ƙasashen ƙetare kuma daga baya a yi ta bautar da su a wuraren damfara.
Ma’aikatar ta ce ta damu matuƙa gama da wasu ‘yan Nijeriya da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Ghana zagon ƙasa (EOCD) ta ‘yanto a Accra babban birnin ƙasar inda aka yi garkuwa da su ana amfani da su wajen damfarar mutane ta intanet a cikin wani mawuyacin hali.
“Ma’aikatar ta gargaɗi ‘yan Nijeriya, musamman matasa, su yi taƙa-tsantsan sosai idan aka yi musu tayin aiki musamman waɗanda ke alƙawarin samun kuɗi cikin sauƙi da fita ƙasashen ƙetare ko kuma aiki mai alaƙa da kirifto daga nesa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce saboda haka ma’aikatar tana bai wa ‘yan Nijeriya shawarar tantance duk wani tayin aiki ta hanyar hukumomin gwamnati tare da ba da rahoto game da duk wani irin tayin da ba su yarda da shi ba saboda hukumomi su yi bincike a kai domin daƙile masu aikata laifuka.
“Wannan lamarin ya nuna tsananin ci-da-gumi da kuma tozartarwa da ke tattare da laifukan da ake aikatawa ta intanet. Ya kuma nuna muhimmancin ingantattun matakai na yaƙar irin waɗannan ƙungiyoyin masu aikata laifuka na biliyoyin daloli da kuma rage sauƙin shigar matasa hannayensu,” in ji sanarwar.
Kazalika, ma’aikatar ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za ta ɗauki matakin rigakafi na magance wannan matsalar, kuma tana aiki da hukumomi a yankin da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa wajen daƙile wannan aika-aikar.
Kwanan nan dai ana samun ‘yan Nijeriya da ke ƙorafin cewa an kai su aiki ƙasashen waje ba tare da ganin abin da aka yi musu alƙawari ba.
