Connect with us

Featured

Nadin Sarautar Galadiman Kano

Sarki Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin Galadiman Kano, yayin da shi kuma Sarki Aminu Ado Bayero ya naɗa Alhaji Sanusi (Lamiɗo) Ado Bayero sarautar ta Galadiman Kano a ranar Juma’ar nan.

An naɗa Alhaji Munir Sanusi a fadar sarki ta Gidan Rumfa inda Sarki Sanusi yake zama, yayin da aka naɗa Alhaji Sanusi (Lamiɗo) Ado Bayero a fadar sarki ta Gidan Nasarawa, inda Sarki Aminu yake zama.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yana daga manyan baƙin da suka halarci naɗin sarautar a Gidan Rumfa.

Lamarin ya ƙara fito da girman rabuwar kan da ake samu a gidan sarautar Kano, inda Sanusi da Aminu kowanne yake da’awar kasancewa halastaccen sarkin na Kano.

A yanzu haka dai batun yana gaban kotuna, inda ake fatan tantance halastaccen sarkin.

 

Yadda Sarki Sunusi Ya Nada Sabon Galadiman Kano

 

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin Turakin Kano; Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano; da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano.

 

Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarki Sanusi ya buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman da su kasance masu koyi da shugabanni da kuma ci gaba da kare martabar sarautar, tawali’u da tausayi ga jama’a.

 

“An zaɓo ku ne bisa la’akari da tarihinku da na iyalan ku, mafi yawanku kun nuna biyayyar ku ga Masarautu da zuriyarmu kuma kun bayar da gudunmawa sosai wajen tallafa wa talakawa da ci gaban al’umma, ina roƙonku da ku yi koyi da magabatanku, Allah Ya yi muku jagora wajen gudanar da ayyukanku,” in ji shi.

 

Taron wanda ya gudana a fadar Sarkin ranar Juma’a ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ’yan majalisar zartarwa na jiha da shugabannin gargajiya da na addini da ’yan uwa da sauran masu faɗa a ji.

 

A wani lamari makamancin haka, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, shi ma ya naɗa Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin Galadiman Kano a ƙaramar fadar Nassarawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet