Featured
Kebbi: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 10
Wasu mahara da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari a ƙauyen Waje da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi, inda suka kashe manoma 15, sannan suka jikkata mutum uku, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Tafida, wanda ya wakilci gwamnan jihar, Nasir Idris a wajen ta’aziyar rashin, ya bayyana takaicinsa kan kisan, sannan ya sanar da tallafin da gwamnatin jihar za ta ba iyalan waɗanda abun ya shafa.
Hakimin Waje, Bala Danbaba ya yaba da zuwan wakilin gwamnatin jihar, sannan ya yi godiya bisa tallafin rage raɗaɗin da gwamnatin ta bayar.
Ya ce ƙaramar hukumar na da iyaka da jihohin Neja da Zamfara da Sokoto, wanda a cewarsa hakan ya sa take fuskantar hare-hare, sannan ya buƙaci a ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro domin kare kwarorowar mahara jihar.
Shugaban ƙaramar hukumar Danko Wasagu Hussaini Aliyu Benea ne ya tabbatar da cewa kashe musu manoma 15, da kuma jikkata guda uku.
