Featured
Eid-el-Kabir: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 6 ga Yuni, da Litinin, 9 ga Yuni, 2025, a matsayin ranakun hutu don bikin Eid-ul-Adha na wannan shekara.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Gwamnatin Tarayya a yau Litinin 02 ga Yuni, 2025.
Ministan ya taya dukkan Musulmi mazauna Najeriya da wadanda ke waje murnar wannan lokaci, tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da nuna sadaukarwa, biyayya da imani kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S) ya yi.
Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na Eid wajen yin addu’ar zaman lafiya da cigaba mai dorewa ga Najeriya baki-daya.
