Connect with us

Featured

NSCDC Ta Musanta Zargin Da Hannunta A Kisan Ɗan Daba a Kano

Biyo bayan harin da aka kai ofishinta na Semegu a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, rundunar NSCDC ta jihar Kano ta yi karin haske kan abin da ya faru.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi, a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Laraba 04 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta ce, “A ranar Litinin, 2 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 8 na dare, wasu mutane biyu dauke da wukake sun yi yunkurin kwace waya a Gwazaye, karamar hukumar Kumbotso. Daya daga cikin ‘yan daban ya kai wa wani mazaunin yankin hari lokacin da yake waya”.

“A cewar ganau, wani dan kungiyar vigilante ya shiga tsakani. Yayin da dan daban ke kokarin kwace wayar, inda kuma aka lakaɗa masa duka, aka kuma soka masa wuka a wuya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.”

“Wanda abin ya faru a kansa tare da wasu makwabtan sa uku, sun garzaya zuwa ofishin NSCDC da ke Semegu, Kumbotso, domin bayar da rahoto.”

“Amma abin takaici, wasu bata-gari dauke da makamai sai suka kai wa ofishinmu hari, suna zargin cewa jami’anmu ne suka kashe dan daban.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa babu wani jami’in NSCDC da ya shiga cikin rikicin.

“Domin kaucewa rudani, muna kara tabbatarwa cewa babu wani jami’inmu da ya shiga wannan rikici. Wadanda suka kawo rahoton satar wayar ne kawai aka kai wa hari tare da jami’anmu,” in ji Abdullahi.

Haka kuma, ya karyata jita-jitar cewa jami’an NSCDC ne suka kashe dan daban.

“NSCDC ba ta kashe ko raunata wani dan daba a yankin ba. Don tabbatar da gaskiya, yanzu haka ‘yan sanda sun dauki nauyin binciken lamarin ta hanyar CID na Kano,” a cewar sanarwar.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet