Featured
Ambaliyar Ruwa : Gwamnatin Neja Ta Dakatar Da Gudanar Da Bukukuwan Sallah A Jihar
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya dakatar da dukkan bukukuwan Sallah na gargajiya, ciki har da Hawan Bariki, Durbar, da sauran tarukan jama’a.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya fitar a ranar Laraba 04 ga Yuni 2025, an bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa Mokwa, wadda ta yi sanadiyyar raba mutane da dama da muhallansu, yayin da ta bar wasu cikin alhini.
“An dauki wannan mataki ne a matsayin girmamawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Mokwa,” a cewar sanarwar.
Gwamna Bago ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummomin da abin ya shafa tare da kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokaci mai alfarma na Eid wajen yin addu’o’i ga mamatan, bayar da sadaka, da nuna jinkai ga wadanda ke cikin mawuyacin hali.
Sanarwar ta kara da cewa, game da Durbar kuwa, wanda a kullum yake daga cikin manyan abubuwan nishadi na Sallah, tare da faretin dawaki da al’adun gargajiya, ba za a gudanar da shi wannan shekarar ba. Soke wannan bukukuwa ya nuna yadda gwamnatin ta fi mayar da hankali kan taimakon al’umma maimakon shagulgulan gargajiya.
