Featured
Dalibai 50 Sun Kubuta Daga Hannun Ƴanbindiga a Neja – CAN
Dalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace a makarantar St. Mary’s Secondary and Primary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara a Jihar Neja, sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane tare da komawa ga iyalansu. Masu garkuwa sun kai hari makarantar da safiyar Juma’a, inda suka harbi mai gadin makarantar sannan suka yi awon gaba da fiye da ɗalibai 200 da kuma ma’aikata 13.
Shugaban CAN na Jihar Neja, kuma mai mallakar makarantar, Mafi Girma Rev. Bulus Dauwa Yohanna, ya tabbatar da faruwar lamarin. A baya ya bayyana cewa dalibai 215 da ma’aikata 12 aka sace, kafin daga bisani ya ce akwai ƙarin dalibai 88 da ba a gano inda suke ba. Sai dai a wata sanarwa daga mai taimaka masa, Daniel Atori, ya tabbatar cewa ɗalibai 50 sun tsere ranar Asabar, kuma yanzu sun haɗu da iyalansu.
A halin da ake ciki, Rev. Yohanna ya ce makarantar tana da dalibai 430 a aji na firamare, inda 377 ke zaman makarantar kwana, 53 kuma daliban yau da kullum ne. Ya ƙara da cewa bayan waɗanda suka dawo, akwai dalibai 141 da ba su shiga cikin waɗanda aka sace ba. A yanzu haka, dalibai 236, yara 3 na ma’aikata, daliban sakandare 14 da ma’aikata 12 na nan a hannun masu garkuwa. A cewar hukumomi, jami’an tsaro na ƙaruwa da kokarinsu don ceto ragowar waɗanda ke tsare.
Kakaki24 na ci gaba da bibiyar lamarin domin kawo sabbin bayanai kan yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikin ceto da kuma martanin hukumomi kan tsaron makarantun yankin.
