Featured
Fiye Da Mutane Miliyan 24 Ne Suka Kamu Da Maleriya a Najeriya – Gwamnatin Tarayya
A wani sabon rahoto da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fitar, fiye da mutum miliyan 24.4 aka tabbatar sun kamu da cutar Malariya a watanni tara na farko na shekarar 2025. Rahoton, wanda ya fito daga 2025 National Health Statistics, ya nuna cewa adadin mutanen da aka yi wa gwajin Malariya ya karu daga zangon farko zuwa na uku, musamman a lokacin damina da kwari ke yawaita.
Kididdigar ta bayyana cewa daga Janairu zuwa Maris an yi wa mutane miliyan 10.5 gwaji, daga Afrilu zuwa Yuni suka zama miliyan 11.4, yayin da daga Yuli zuwa Satumba suka karu zuwa miliyan 12.8. Daga cikin waɗannan, sama da miliyan 7.3 sun fito da sakamakon Malariya a zangon farko, miliyan 7.8 a na biyu, sannan miliyan 9.3 a zangon uku — wanda ya kai jimillar da ta haura miliyan 24.46.
A cewar Kakaki24, masana sun ce matsalar ta samo asali ne daga jinkirin neman magani, ƙarancin kayayyakin kiwon lafiya da kuma yawaitar kwari a lokacin damina. Rahoton ya kuma ce sama da miliyan 23.8 ne aka yi wa magani da Artemisinin-based Combination Therapy (ACT) a wannan lokacin, adadin da ya yi daidai da yawan sabbin kamuwa da cutar.
Ministan Ƙasa na Lafiya, Dr. Iziaq Salako, ya ce Shirin Kula da Malariya na ƙasa ya sami gagarumin nasara, musamman wajen inganta gwaji da wuri da kuma samun isassun magunguna ga marasa lafiya. Ya ce gwamnati na ƙara zage damtse don rage yaduwar cutar kafin ƙarshen shekarar 2025.
