Featured
Kamfaninmu Ya Biya Harajin Naira Biliyan 450 A Shekarar 2024 – Dangote
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa kamfanonin rukunin Dangote sun biya harajin Naira biliyan 450 a shekarar 2024, wanda ya sanya shi zama kamfanin da ya fi biyan haraji a Najeriya. Wannan haraji da kamfanonin Dangote suka biya ya zarce wanda dukkan bankuna Najeriya suka biya idana aka hadasu baki daya.
Dangote ya kara da cewa, duk da wannan haraji da ya biya a bara, rukunin Dangote zai kashe karin Naira biliyan 900 wajen gyaran hanyoyin mota a fadin Najeriya. Dangote ya bayyana cewa hanyar shiga tashar ruwa ta teku mai zurfi (Deep-Sea Port Access Road) tana daga cikin hanyoyi da rukunin Dangote ke ginawa a karkashin tsarin bayar da bashin haraji na gwamnatin tarayya.
A cewar Dangote, hanyar tashar ruwa ta teku “tana cikin manyan hanyoyi guda takwas da suka kai jimillar tsawon kilomita 500, ciki har da hanyoyi biyu a Jihar Borno da za su hada Najeriya da kasashen Chadi da Kamaru.”
Ya kuma yabawa shugabancin Shugaba Tinubu, inda ya bayyana shi a matsayin jagora mai jarumtaka wanda ya dawo da kwarin gwiwa ga masu zuba jari daga sashen masu zaman kansu.
Dangote ya kuma godewa shugaban kasa bisa hangen nesan da ya yi wajen aiwatar da aikin tashar ruwa ta teku ta Lekki, sannan ya tabbatar masa da goyon bayan sashen masu zaman kansu wajen fadada hanyoyin sufuri a fadin kasar.
Dangote ya kuma bayyana cewa hanyar da za ta kai zuwa masana’antar Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals za’a sanya mata suna “Bola Ahmed Tinubu Road” a matsayin girmamawa ga Shugaba Tinubu.
