Connect with us

Featured

Cristiano Ronaldo Ya Tabbatar Da Cewa Zai Cigaba Da Zama a Al Nassr a Kaka Mai Zuwa

Dan wasan gaba na Portugal, Cristiano Ronaldo, ya shirya tsawaita zamansa tare da kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a Saudiyya, inda kuma yake shirin sanya hannu a sabuwar yarjejeniya.

A cikin wani rubutu da Fabrizio Romano ya wallafa a X ranar Litinin 09 ga Yuni 2025, dan wasan ya karyata jita-jitar cewa zai bar Al Nassr.

Rubutun ya ce, “Cristiano Ronaldo ya tabbatar da shirin cigaba da zama a Al Nassr ta hanyar sanya hannu a sabuwar yarjejeniya.

“Makomata? A zahiri, babu wani canji. Zama a Al Nassr? Eh.”

A ranar Lahadi 08 ga Yuni 2025, Dan wasan mai shekaru 40 ya taimaka wa kasar sa wajen lashe gasar Nations League karo na biyu a cikin shekaru hudu bayan kaddamar da gasar.

Ronaldo, wanda ya koma Al Nassr a watan Disamba 2022 a kan yarjejeniya mai tarihi, ya taka rawa mai matukar muhimmanci a kungiyar, a ciki da wajen fili.

Zuwan Ronaldo ya zama wani abun alfahari ga kwallon kafar Saudiyya, kuma ya jawo hankalin duniya zuwa gasar Saudi Pro League, kuma ya sa wasu fitattun ‘yan wasa suka shiga gasar.

A cikin lokaci da ya shafe a Al Nassr, Ronaldo ya nuna bajinta, yana yawan zura kwallaye kuma yana taimaka wa kungiyar wajen kasancewa a matakin gasar. Zuwa yanzu, kasancewar Ronaldo a kungiyar ya kara daukaka martabar kungiyar da kuma bunkasa shaharar gasar a fadin duniya.

Sanarwar cigaba da zaman Ronaldo a Al Nassr ana kallonta a matsayin babban karin karfi ga kungiyar da kuma gasar Saudi Pro League baki daya. Wannan kuma yana nuna kudirin Ronaldo wajen cigaba da kasancewa a cikin wannan gagarumin aikin bunkasa kwallon kafa a yankin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet