Connect with us

Featured

Masu Bawa Tinubu Shawara Yaudararsa Suke Su Na Ɓata Masa Suna – Ndume

Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya zargi hadiman shugaban kasa, waɗanda ya kamata a ce suna taimaka wa Shugaba Bola Tinubu, amma su ne suke da yaudararsa kan al’amuran kasa.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikinsu suna ɓata masa suna ne kawai.

Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Lahadi 08 ga Yuni 2025. Ya ce wasu daga cikin muhimman mutanen da ke kusa da Tinubu suna tafiyar da al’amura bisa son rai ne da kuma rashin ƙwarewa.

“Ina ganin akwai mutane da suke yaudarar shugaban kasa, suna gaya masa abin da yake son ji”.

“Ni abinda nake gani shi ne, waɗanda Tinubu ya dogara da su, su ne suke yaudararsa kuma su ke ɓata masa suna,” inji Ndume.

“Waɗannan mutane basuda gaskiya. Na faɗa a baya kuma ba zan canja matsayina ba, sai dai idan sun gyara ko shugaban ƙasa ya dauki mataki.

Duk da cewa ya ƙi bayyana sunayen wadanda yake nufi, Ndume ya bayyana cewa ɓarnar da ake yi a bayyane take kuma tana da muni sosai.

Sanatan ya kuma soki yadda shugaban kasa da muƙarrabansa suka kasa ganin irin wahalar da jama’a ke fama da ita sakamakon manufofin tattalin arziki.

“Shugaban kasa ba zai iya fita titi kamar yadda nake yi ba don ya ga yadda jama’a ke ji.

“Ko gefen fadar shugaban kasa, rufe masa gilasan mota su ke da baƙin gilashi, saboda kada ya ga abinda yake faruwa.

“Jama’a su na cikin damuwa, shi kansa shugaban kasa yasan haka. Ya kuma yadda akwai matsaloli, shiyasa ma yake rokon al’umma su ƙara hakuri,” inji Ndume.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet