Connect with us

Featured

Tinubu Zai Yi Jawabi Ga Ƴan Najeriya a Gobe Alhamis

Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke bikin faretin soja na gargajiya da aka saba gudanarwa duk shekara, domin bikin cika shekaru 26 na ranar Dimokuradiyya a ranar Alhamis, 12 ga Yuni, 2025.

Ba a bayar da wani dalili a hukumance game da soke faretin sojan ba.

A maimakon haka, Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga kasa baki daya da karfe 7 na safe ranar Alhamis, kamar yadda wata sanarwa da Kwamitin Hadin Gwiwa na Bikin Ranar Dimokuradiyya ya fitar a yau Laraba 11 gabYuni, 2025.

Shugaban kasar zai kuma halarci wani zama na musamman na hadin gwiwa na Majalisa a Alhamis din, da misalin karfe 12 na rana. Ana sa ran wannan zaman zai tattauna kan manyan nasarorin da dimokuradiyya ta yi.

Sanarwar da Abdulhakeem Adeoye ya sanya wa hannu a madadin Daraktan Sashen Labarai da Hulɗa da Jama’a a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ta bayyana sabbin tsare-tsare.

Ta ce, “Kwamitin Hadin Gwiwa yana sanar da sabbin tsare-tsare kamar haka don bikin cikar shekaru 26 na ranar Dimokuradiyya:

1. Jawabin Shugaban Kasa ga yan Najeriya a ranar 12 ga Yuni, 2025 da karfe 7 na safe.

2. Babu faretin ranar Dimokuradiyya.

3. Mai Girma Shugaba Bola Tinubu zai halarci zaman hadin gwiwa na Majalisar kasa da karfe 12 na rana.

4. Taron karatu kan bikin ranar Dimokuradiyya a dakin taro na State House, Abuja. Lokaci: 4 na yamma.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet