Connect with us

Featured

Mutum Ɗaya Ya Tsira, Bayan Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane 242 Ya Yi Hatsari a India

Jirgin Air India mai lamba 171 wanda ya nufi London, ya faɗi ne a wata unguwa da ke kusa da filin jirgin sama a birnin Ahmedabad, ranar Alhamis, 12 ga Yuni, 2025, inda ake kyautata zaton dukkan mutanen ciki 242 sun mutu, jirgin ya faɗa kan wasu gine-ginen da ke dauke da likitoci da iyalansu.

Wani ɗan jaridar AFP ya ga yadda ake ciro gawawwaki daga wurin da hatsarin ya faru.

Firayim Minista Narendra Modi ya bayyana cewa, “Hatsarin da ya faru a Ahmedabad ya girgiza mu matuƙa. Zuciyarmu ta cika da baƙin ciki.”

Kwamishinan ‘yan sandan birnin, GS Malik, ya ce an riga an gano gawawwakin mutane 204, ciki har da na fasinjoji da wadanda hatsarin ya rutsa da su a ƙasa, yayin da aka kwantar da wasu da suka jikkata a asibiti.

A baya an yi zaton cewa dukkan fasinjoji sun mutu, amma jami’in lafiya na jihar, Dhananjay Dwivedi, ya shaida wa AFP cewa “akwai mutum ɗaya da aka tabbatar ya tsira” kuma yana samun kulawa a asibiti.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Indiya ta ce mutane 242 ne ke cikin jirgin — ciki har da matuka biyu da ma’aikata10.

Air India ta bayyana cewa akwai fasinjoji 169 ‘yan Indiya, 53 Birtaniyya, 7 ‘yan Portugal, da ɗan ƙasar Kanada guda ɗaya a cikin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin Gatwick na birnin London.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet