Featured
Rikici Kan Budurwa Ya Yi Ajalin Wani Ɗan Najeriya a India
‘Yan sandan ƙasar Indiya sun kama wasu ‘yan Najeriya biyu, Chukwudi Okafor (31) da Samuel Eze (34), bisa zargin kashe abokinsu Emeka Christian, sakamakon rikici kan wata mata a birnin Pune. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin a yankin Pisoli-Phursungi, kamar yadda India Today ta ruwaito.
Rahoton ya ce marigayin, mai shekaru 40 yana zaune ne bisa a India bisa ƙa’ida da doka, inda ya halarci wani ƙaramin taro a gidan wata ‘yar Najeriya a daren Lahadi. A nan ne wani rikici ya faru bayan wani sabani kan alaƙar soyayya da matar, inda muhawarar ta rikide zuwa fada.
‘Yan sanda sun bayyana cewa an bugawa Emeka wani abu mai ƙarfi yayin da yake ƙoƙarin barin gidan da misalin ƙarfe 3:00 na safe, lamarin da ya jawo masa munanan raunuka. Nan take aka kai shi asibiti amma aka tabbatar da rasuwarsa, yayin da aka kama waɗanda ake zargi tare da ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin.
