Featured
Fiye Da Mutane 100 Ne Su Ka Mutu A Wani Sabon Harin Ƴan Bindiga A Yelewata, Jihar Benue
Aƙalla mutane 100 ne ake fargabar sun rasa rayukansu a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Yelewata da ke karamar hukumar Guma a Jihar Benue.
Harin ya auku ne da safiyar Asabar din nan 14 ga Yuni, 2025.
DailyTrust ta rawaito cewa, a wani hari daban da ya auku a garin Daudu, wanda shima ke cikin karamar hukumar Guma, yayi sanadiyar mutuwar wasu sojoji biyu.
Wannan harin dai shine karo na uku cikin mako guda da aka kai garin Yelewata, wani ƙauye da ke kan iyakar Benue da Nasarawa, yayin da Daudu kuma ke tazarar mintuna 20 daga Makurdi, babban birnin jihar.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun iso Yelewata da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare, inda suka yi kaca-kaca da garin fiye da tsawon sa’o’i biyu ba tare da wani agaji daga jami’an tsaro ba.
A baya, wasu samari mazauna yankin suna ƙoƙarin kare garin, amma wannan karon sun zo da yawa kuma dauke da makamai na zamani, suka rinjayi kowa,” in ji wani mazaunin yankin.
Wani ma’aikacin karamar hukumar Guma da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce wannan harin tamkar yunkuri ne na kawar da wani yanki gaba ɗaya. “Fiye da gawarwaki 100 aka riga aka gano, kuma an kone wasu iyalai har sun gaza ganewa,” in ji shi.
“Yawancin waɗanda abin ya rutsa da su ‘yan gudun hijira ne da ke kwana a cikin rumfuna da shagunan kasuwa. Wadannan miyagun sun zuba mai suka ƙona su da rana. Suka kutsa cikin gidajen mutane, suka sare su da takubba.”
Kakakin Rundunar Ƴan Sanda na Jihar Benue, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar lamarin na Yelewata, sai dai bai bayyana adadin mutanen da suka mutu ba.
Ya ce, “A cewar bayanan da muka samu, harin ya faru ne a safiyar yau (Asabar), inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Yelewata. Rundunar ‘yan sanda da tawaga ta musamman da ke yankin sun amsa kiran gaggawa tare da fuskantar maharan, kuma an kashe wasu daga cikinsu.”
“Amma abin bakin ciki ne cewa wasu mutane sun rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka jikkata. Rundunar ‘yan sanda na ci gaba da kokari don kama maharan da tabbatar da tsaron jama’a,” a cewar sa.
