Featured
Matsalar tsaro na neman mayar da Najeriya tamkar wani sansanin ƴan gudun hijira – Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce kashe-kashe da hare-haren da ake fama da su a Najeriya na neman mayar da ƙasar tamkar wani sansanin ‘yan gudun hijira.
Obi ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci wata al’umma da aka kai wa hari a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau, domin jajanta wa mutanen da rikicin tsaro ya raba da gidajensu. Ya ce gwamnati ta gaza samar da isasshen tsaron da zai ba wa ƴan gudun hijirar damar komawa garuruwansu.
Read Also : Batun addini ne ke taka rawa a shari’ar El-Rufai – Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar kashe-kashe da satar mutane da ke tilasta wa al’ummomi barin gidajensu, musamman a Plateau da Benue. Obi ya ce gwamnati na da alhakin kare jama’a tare da hukunta waɗanda ke kai hare-hare.
Obi ya ce kimanin mutane 45,000 daga al’ummomi sama da 20 ne suka rasa matsugunansu. Ya kuma nuna damuwa kan yadda rikicin ke hana yara zuwa makaranta, tare da tabbatar wa shugabannin sansanin cewa zai ci gaba da tallafa musu gwargwadon ƙarfinsa.
