Featured
Tinubu ya karbi shugabancin Najeriya a lokacin da take dab da durƙushewa – Gwamnan Filato
Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaji Najeriya ne a lokacin da tattalin arzikinta ke dab da durkushewa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC a Jos.
Ya ce a lokacin da Tinubu ya karbi mulki, Najeriya ba ta iya biyan basussukan kasashen waje, yayin da gwamnati ta koma buga kudi domin tafiyar da tattalin arzikin kasa. Ya kuma ce ajiyar kudaden kasashen waje ta ragu zuwa sama da dala biliyan uku.
Gwamnan ya ce a yanzu ajiyar kudaden kasashen waje ta haura dala biliyan 50, sannan man fetur ya samu a kasuwa, duk da cewa farashinsa bai yi sauki ba. Ya kuma tuna da lokacin da ‘yan Najeriya ke shafe kwanaki suna layin gidajen mai domin samun man fetur.
Mutfwang ya ce yana da yakinin cewa Plateau za ta bai wa Tinubu gagarumar nasara a zaben 16 ga Janairu, 2027. Ya kuma bukaci magoya bayan APC su koma yankunansu domin wayar da kan al’umma da kuma tattara kuri’u.
