Featured
Kotu Ta Bayar Da Belin Sanata Natasha Akan Naira Miliyan 50
A Alhamis din nan 19 ga Yuni, 2025. Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ta bayar da belin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar daga wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, bisa sharadin biyan naira miliyan 50 da kuma kawo mutum daya da zai tsaya mata, wanda dole ne ya kasance mai kwarjini, yana zaune a Abuja kuma wanda ya mallaki fili a cikin karamar hukumar birnin tarayya (AMAC).
Mai shari’a Chizoba Orji ce ta yanke hukuncin bayan sauraron muhawara daga lauyoyi kan bukatar bayar da belin.
Tun da farko an zargi Natasha da aikata kalaman batanci kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yayin wani shirin gidan talabijin na Channels TV mai suna Politics Today a ranar 3 ga Afrilu, 2025.
A cikin karar, an bayyana cewa Natasha ta zargi tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da Sanata Akpabio da yin shirin kisa a kanta a wajen birnin Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta ce Sanata Natasha ta san wannan kalami zai iya cutar da martabar Akpabio.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa an tsara gurfanar da Natasha a ranar 3 ga Yuni, 2025, amma yajin aikin ma’aikatan shari’a ya hana faruwar hakan.
