Featured
Rasha Ta Ja Kunnen Amurka Kan Shiga Yaƙin Isra’ila Da Iran
Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar TASS cewa shigar Amurka cikin yaƙin Isra’ila da Iran ka iya haifar da ”mummunar ƙazancewar yaƙin”.
Amurka da Rasha na goyon bayan ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna.
Yayin da Donald Trump ya buƙaci Iran ta “miƙa wuya ba tare da sharadi ba”, kuma rahotonni ke cewa yana duba yiwuwar kai mata hari, ita kuwa Rasha na kallon Iran a matsayin babbar ƙawa.
A farkon wannan shekarar ne, Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata ƙawance mai ƙarfi da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, inda wani ɓangare na yarjejeniyar ya buƙaci ƙulla ƙawancen tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Haka kuma Iran na samar wa Rasha jirage marasa matuƙa, da suka taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ƙasar ke yi da Ukraine.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta yi Allah wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran, haka kuma jiya mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar ya gargaɗi Amurka da kada ta bai wa Isra’ila taimakon soji.
“Saboda hakan zai iya dagula yanayin da ake ciki,” kamar yadda ya bayyana.
Da alama rikicin zai haifar da cin karo tsakanin Rasha da Amurka, kuma zai iya zama babbar barazana a dangantakar Amurka da Rasha, wadda ta ɗan fara inganta bayan sake zaɓar Donald Trump.
