Featured
Isra’ila da Hamas Sun Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Gaza
Bayan doguwar tattaunawa a Masar, Isra’ila da Hamas sun amince da matakin farko na wani shiri da nufin kawo karshen yaƙin da ya daɗe yana ci a Gaza. Wannan mataki ya ƙara hasashen samun zaman lafiya mai ɗorewa bayan shekaru biyu na rikici.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya sanar da wannan ci gaba, inda ya bayyana shi a matsayin “babbar rana ga duniya” da kuma matakin farko na tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yarjejeniyar ta haɗa da tsagaita buɗa wuta, sakin dukkan Isra’ilawa da Hamas ke garkuwa da su, da kuma sakin Falasɗinawa da Isra’ila ke tsare da su. Haka kuma Isra’ila za ta fara janye dakarunta daga yankin Gaza a mataki na farko.
Trump ya shaida wa kafar Fox News cewa a ranar Litinin za a fara sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, matakin da ake ganin zai ba da sabuwar dama ga ci gaban tattaunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.
