Connect with us

Featured

Mutane Miliyan 139 Na Rayuwa Cikin Talauci a Najeriya – Bankin Duniya

Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa Najeriya har yanzu na cikin matsanancin talauci duk da cewa tattalin arziƙinta ya samu ɗan bunƙasa a cikin ‘yan watannin baya. Bankin ya ce gyare-gyaren tattalin arziƙin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar ba su rage yawan talauci a ƙasar ba. A cewar bankin, sama da mutane miliyan 139 ne ke rayuwa cikin talauci a shekarar 2025.

Daraktan ƙasa na Babban Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da rahoton cigaban Najeriya. Ya ce duk da hasashen cewa tattalin arziƙin ƙasar zai bunƙasa da kashi 4.4 cikin 100 nan da shekarar 2027, har yanzu matsalar talauci da rashin daidaito a rarraba arziƙi na ci gaba da ta’azzara.

Verghis ya bayyana cewa manufofin gyare-gyaren da gwamnati ke aiwatarwa suna da muhimmanci wajen farfaɗo da tattalin arziƙi, amma ba su kai ga inganta rayuwar miliyoyin ‘yan ƙasa ba. Ya ce akwai buƙatar ƙarin matakai da za su shafi rayuwar talakawa kai tsaye, musamman a fannoni kamar ilimi, lafiya da samar da ayyukan yi.

Wannan rahoto na Babban Bankin Duniya ya biyo bayan jawabin Tinubu a bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya yaba wa gwamnatinsa bisa abin da ya kira “sake farfaɗowar tattalin arziƙin ƙasa.” Sai dai sakamakon bankin ya nuna cewa har yanzu akwai babban gibi tsakanin manufofi da tasirin su a rayuwar jama’a.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet