Connect with us

Featured

Isra’ila Ta Cigaba Da Luguden Wuta a Gaza Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a Gaza a daren Juma’a duk da kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tsagaita wuta, bayan ƙungiyar Hamas ta amince da shirin tsagaita wutar da aka gabatar. Hukumar kashe gobara ta Gaza ta tabbatar da cewa hare-haren sun fi karkata ne kan Gaza da wasu sassan yankin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da rudani.

Mai magana da yawun hukumar ceto ta Gaza, Mahmud Bassal, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa daren ya kasance “mai tsananin tashin hankali,” inda jiragen yaki da manyan bindigogi na Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a yankuna da dama. Ya bayyana cewa gidaje 20 aka rushe, sannan ayyukan ceto sun yi wuya saboda kasancewar tankunan Isra’ila a yankin da kuma cigaban harin.

Asibitin Baptist da ke Gaza ya tabbatar da cewa ya karɓi gawarwaki da raunatattu daga wani harin da ya auku a unguwar Tuffah, ciki har da mutum huɗu da suka mutu. Haka kuma, asibitin Nasser da ke Khan Yunis, a kudancin Gaza, ya ce yara biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da mutane takwas suka ji rauni sakamakon harin jirgin ɗan tashi a sansanin ‘yan gudun hijira.

Wannan na zuwa ne bayan da Trump ya gabatar da sabon shirin zaman lafiya wanda Isra’ila ta amince da shi, wanda ya haɗa da tsagaita wuta, sakin fursunonin da Hamas ke rike da su cikin awanni 72, sauke makaman Hamas da kuma janye dakarun Isra’ila a hankali daga Gaza. Hamas ta bayyana shirinta na sakin wasu daga cikin fursunonin bisa tsarin shirin, amma ta nemi a tattauna kan cikakkun bayanai da kuma rawar da zata taka a makomar yankin Falasɗinu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet