Featured
Sabbin Hare-Hare Sun Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 59 A Jihohin Borno, Kano, Kebbi da Filato
Aƙalla mutane 59 ne suka mutu a wasu mabanbanta hare-hare da suka auku a jihohin Borno, Kano, Kebbi da Filato a ranar Juma’a 20 ga Yuni, da Asabar 21 ga Yuni, 2025.
Mutane 30 aka kashe a jihar Kebbi, yayin da wasu 12 da aka bayyana a matsayin baƙin biki suka mutu a jihar Filato. A jihar Borno kuma, mutum 12 sun rasa rayukansu a wani harin bam da wata mace ta kai a kasuwar kifi. A Kano kuwa, wani bam na soja ya tashi a unguwar Eastern Bypass, ya hallaka mutane biyar.
Mutum 12 sun mutu a harin kunar bakin wake a Borno
Wasu mazauna ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno sun bayyana cewa wata mace ce ta tayar da bam ɗin inda ta kone kurmus.
An bayyana cewa waɗanda suka jikkata a harin an garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
“Wajen kasuwa ne inda mutane ke cin abinci da sayayya. Komai yana tafiya lafiya sai kawai muka ji ƙarar fashewa. Da dama sun mutu,” in ji wani shaidan gani da ido.
An binne gawarwakin mutanen da suka mutu a ranar Asabar 21 ga Yuni 2025. Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Konduga.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da harin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a, Nahum Daso, inda ya ce harin ya faru da misalin karfe 9:30 na dare ranar Juma’a 20 ga Yuni, 2025.
Bam ya hallaka mutane 5 a Kano
A jihar Kano kuwa, wani bam da ake kyautata zaton na sojoji ne ya tashi a cikin wata mota da ke ɗauke da kaya daga jihar Yobe.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Bakori, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa mutane biyar sun mutu, yayin da goma ke karɓar magani a asibiti.
Ya ce bincike yana gudana kuma yana neman hadin kai da kwanciyar hankali daga jama’a domin samun cikakken bayani kan lamarin.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 30 a Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 30 a wasu hare-haren ‘yan bindiga da suka auku a yankin masarautar Zuru.
Mataimakin Gwamna, Sanata Umar Abubakar Tafida, ne ya jagoranci tawagar zuwa garuruwan Tadurga da Kyebu don yin ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Ya ce gwamnati za ta ƙara tsaurara matakan tsaro da kuma toshe hanyoyin da ‘yan ta’adda ke bi suna kutsa wa garuruwan.
Gwamnati ta bada tallafin Naira miliyan 50 domin taimakon iyalan mamatan da gyaran garuruwan da lamarin ya shafa.
Matasa sun kashe baƙin biki 12 a Filato
Rundunar ‘yan sanda a Filato ta ce ta kama mutane 22 bisa zargin hannu a kisan baƙin biki 12 da aka kashe a kauyen Mangun, karamar hukumar Mangu.
Mai magana da yawun rundunar, Alfred Alabo, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Asabar 21 ga Yuni, 2025.
Wadanda aka kashe na cikin motar haya mallakar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Sun fito ne daga Zaria zuwa garin Qua’an Pan domin halartar biki.
Shaidu sun ce da misalin ƙarfe 8 na dare ne suka tsaya don tambayar hanya, sai wasu matasa suka kai musu hari da muggan makamai, suka kashe 12, suka kona motar da wasu gawarwaki a ciki.
Rundunar Lafiyan Jama’a ta ceto waɗanda suka jikkata, inda aka garzaya da su asibiti.
Wani wanda ya tsira, Ibrahim Umar, ya ce: “Mun tsaya muna tambayar hanya sai kawai wasu suka farmake mu. Suka fara da direban, suka kashe shi, suka ci gaba da dukanmu. Suka ƙona motar da gawarwaki a ciki.”
