Featured
Yunƙurin Dauko Wayar Salula A Masai Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano
Wasu mutane biyu, Usman Muhammed da Ibrahim Inuwa, sun rasa rayukansu a ranar Asabar 21 ga Yuni, 2025. Yayin da suke ƙoƙarin ciro waya daga masai a ƙaramar hukumar Albasu, jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a kauyen Bazabe, inda wasu maza biyu, masu shekaru 40, suka gamu da ajalinsu lokacin da su ke ƙokarin ciro wayar salula daga masai.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 22 ga Yuni, 2025.
A cewar sa “Mun samu kiran gaggawa daga wani jami’in mu a Takai Fire station mai suna Auwalu da misalin ƙarfe 11:16 na safe, yana sanar da mu cewa wasu mutane biyu sun fada cikin bayan gida”
“Muka tura ƙungiyar ceto zuwa wurin da abin ya faru domin ceto mutanen.”
Ya bayyana cewa Muhammed ne ya fara fadawa cikin bayan gidan (Masai) yayin da yake ƙoƙarin ciro wayarsa da ta faɗa ciki.
“Daga nan sai Inuwa ya ɗaura igiya a jikinsa, ya shiga bayan gidan da nufin ceton Muhammed, amma shi ma ya makale.”
A cewarsa, an fito da su daga bayan gidan cikin mawuyacin hali, kuma nan take aka garzaya da su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Ya ƙara da cewa tuni aka sanar da ofishin ‘yan sanda na ƙaramar hukumar Albasu game da lamarin.
