Featured
Yan Sanda A Bauchi Sun Gargadi Matasa Kan Ɗabi’ar Hawa Ƙarfen Sabis Saboda Neman Suna
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta fitar da gargadi ga jama’a, musamman matasa, dangane da wata sabuwar dabi’ar hawa ƙarfen sabis domin kawai neman suna.
A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, SP Ahmed Wakil, ya fitar a ranar Talata 01 ga Yuli, 2025. Ya bayyana cewa wannan mummunar dabi’a ta haifar da wasu abubuwa marasa dadi, wanda hakan ya sa rundunar ta dauki wannan mataki.
Sanarwar ta bayyana cewa an samu rahoton aƙalla mutane guda uku wadanda suka yi yunkurin kashe kansu ta hanyar hawa karfen sabis din.
Wakil ya ce, “Lamari na farko ya faru ne a ranar 16 ga Yuni, 2025, inda wani saurayi mai suna Adamu Salisu, dan shekara 22 da haihuwa wanda aka fi sani da ‘Sarkin Malaman Samarin Kasuwar Muda Lawal’ ya hau karfen sabis da ke kusa da makarantar firamare ta Kofar Dumi.
“Ya bayyana cewa ba zai sauko ba sai Alhaji Bala Wunti ya amsa kiran da yake masa domin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna.”
Na biyu kuwa ya faru ne a ranar 18 ga Yuni, 2025, inda wani mai suna Usman Nanu, dan shekara 35 daga unguwar Kofar Dumi a cikin garin Bauchi, ya hau wani karfen sabis don nuna goyon bayansa ga Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, CON (Kauran Bauchi).
“Ya ce ba zai sauko ba har sai Gwamnan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a 2027.”
Wakil ya ce na baya bayan nan kuwa, ya faru ne a ranar 29 ga Yuni, 2025, inda wani Alkassim Saidu Yakubu, dan shekara 37 daga unguwar Unguwan Magaji Inkil ya hau sabis din MTN.
“Ya bayyana cewa ba zai sauko daga karfen ba sai Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027.”
Jami’in hulda da jama’a ya ce a dukkan wadannan ukun ‘yan sanda sun gaggauta zuwa wuraren, inda suka ceto mutanen cikin koshin lafiya sannan aka tuhumesu da laifin yunkurin kashe kansu.
Ya ce duk wadanda suka yi hakan sun amsa cewa sun aikata hakan ne cikin rashin sani kuma sun nuna nadama, tare da cewa za a bincike su, a dauki bayanansu, sannan a gurfanar da su a gaban doka.
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya nuna damuwa sosai kan wannan sabuwar dabi’a mai hadari da wasu matasa ke aikatawa a jihar.
Ya yi kira ga jama’a da su guji irin wannan mataki mai hadari da zai jefa rayuka cikin hadari, tare da jaddada cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan za a hukunta shi bisa doka.
Kwamishinan ya kuma bukaci iyaye, masu ruwa da tsaki, da shugabanni su rika ba wa matasa shawara da kaurace wa kalaman da ka iya tayar da hankali ko kawo tarzoma a jihar.
Ya kuma ce duk wanda aka samu da hannu ko da a rufa-rufa wajen tayar da hankalin jama’a, za a cafke shi, a bincike shi, sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.
