Featured
Najeriya Na Bukatar Dala Biliyan Ɗaya Don Cigaba Da Shirin Rigakafin Cututtuka – NPHCDA
Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa wato National primary health care development agency ta ce Najeriya na bukatar dala biliyan daya cikin shekaru biyar masu zuwa don tabbatar da ci gaba da shirin rigakafin cututtuka.
Shugaban hukumar, Dr. Muyi Aina ne ya bayyana haka a Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki kan samar da kudin rigakafi mai dorewa.
Ya ce kashi 21 cikin 100 kacal na kasafin kudin rigakafi na bana aka saki, yana mai gargadin cewa hakan na iya kawo koma baya ga nasarorin da aka samu.
A cewar sa “a bana an yi wa yara miliyan uku rigakafi, waɗannan ba su taba samun rigakafi ba, an yi wa ’yan mata miliyan 14 rigakafin cutar sankarar mahaifa, tare da rabon allurai miliyan 91 a fadin Najeriya”.
Gwamnati na kokarin nemo sabbin hanyoyin samun kudade, ciki har da haraji na musamman, don ci gaba da kare lafiyar al’umma.
