Featured
INEC Za Ta Fitar Da Sabbin Ƙa’idojin Duba Sakamakon Zaɓe a Najeriya
A shirye-shiryen da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) take take yi gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, ta bayyana shirin ta na fitar da ƙarin ƙa’idoji da za su jagoranci yadda za’a duba sakamakon zaɓen da aka riga aka bayyana.
Shugaban INEC, farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a taron da hukumar tayi da kwamishinonin zaɓe na jihohi a Abuja.
Farfesa Yakubu ya kuma bayyana damuwa kan yadda mutane ke fassara Sashe na 65 na dokar zaɓe ta 2022. Wanda ke ba INEC damar duba sakamakon zaɓe ta hanyoyi daban-daban, inda ya ce hukumar na aiki kan sabbin ƙa’idoji da za su bayyana yadda ake nazari da sake duba sakamakon zaɓe.
A cewar sa “Sabbin dokokin za su kasance ƙari ne ga dokokin gudanar da zaɓe na 2022, kuma za a wallafa su a shafin hukumar nan bada jimawa.”
Ya kara da cewa INEC ta riga ta gana da shugabannin jam’iyyu da ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida da jami’an tsaro domin samun haɗin kai.
Haka kuma, dukkan jihohin Najeriya da Abuja suna da sabbin kwamishinonin zaɓe masu cikakken iko.
A baya bayan nan hukumar INEC ta sanar da shirinta na gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabu da dama da abin ya shafa, a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta shekarar nan da muke ciki ta 2025.
