Featured
INEC ta sanya sunan Pantami cikin jerin yan takarar gwamna a Gombe
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya sunan Prof. Pantami cikin jerin ’yan takarar gwamnan Jihar Gombe da za su fafata a zaben watan Fabrairun 2027.
A shafin hukumar zaben da DCL Hausa ta bibiya a safiyar Asabar, an ga sunan Pantami tare da Haruna Ahmad, wanda aka sanya a matsayin mataimakinsa.
Read Also : INEC ta fitar da sabon jadawalin yan takarar gwamnan Kano babu sunan Aminu Abdussalam
Sunan Prof. Pantami shi ne na 15 a cikin jerin ’yan takara 19 da za su fafata a zaben gwamnan Jihar Gombe.
Jihar Gombe dai na cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya, inda ’yan takarar za su fafata domin neman kujerar gwamnan jihar a zaben Fabrairun 2027.
