Featured
INEC ta musanta fitar da sanarwa ta musamman kan ƴan takarar gwamna da basu ga sunan su ba
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta fitar da wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da hukumar kan jerin sunayen ƴan takarar gwamna a jihohi shida na Najeriya.
Jihohin sun haɗa da Kano, Zamfara, Gombe, Delta, Plateau da Yobe. Hukumar ta bayyana cewa sanarwar ta bogi ce ba ita ce ta fitar da ita ba, tana mai cewa duk wani bayani da ke nuna cewa ta yi sanarwa ta musamman kan ƴan takarar gwamnan jihohin ƙarya ne.
Read Also : AHIP Calls for Greater Investment in Girls’ Education, Health
INEC ta buƙaci al’umma da su yi watsi da sanarwar tare da guje wa sake yaɗa ta, tana mai kira gare su da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanan zaɓe kafin su amince da su ko su yaɗa su.
Hukumar ta shawarci jama’a da su riƙa samun sahihan bayanai daga shafukanta na hukuma, ciki har da www.inecnigeria.org, shafukan Facebook, X da Instagram, da kuma www.inecnews.com.

Pingback: Ƙididdigar da muka yi ta nuna cewa Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 - APC - KAKAKI 24