Connect with us

Featured

Duk ɗan takarar da INEC ta cire sunansa kada ya ɓata kuɗinsa da lokacinsa wajen zuwa kotu domin ba zai yi nasara ba – Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunayensu daga jerin ’yan takarar zaɓen 2027, da kada su ɓata kuɗi da lokaci wajen shigar da ƙara a kotu.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce hukuncin Kotun Ƙoli da ya ba INEC damar cire sunayen wasu ’yan takara ya fito ƙarara. Ya kuma yi kira ga lauyoyi da manyan lauyoyin ƙasar da su ba waɗanda abin ya shafa shawarar da ta dace.

Read Also : Kano Health Sector Under Abba: From Crisis To Example (2)

Ya ce bai kamata ’yan takarar su ci gaba da kashe kuɗaɗe da ƙarfinsu wajen yaƙin da ya riga ya zama kamar an kayar da su ba, yana mai ba da shawarar su mayar da hankali wajen tsara dabarun siyasar nan gaba maimakon shigar da sabbin ƙarar da ba za su amfane su ba.

Cikin ’yan takarar da sunayensu ba su bayyana a sabon jerin INEC akwai Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, Ladi Adebutu da ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo. Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a ranar 24 ga Satumba, 2026, inda ta tabbatar da wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 tare da amincewa da sabon jadawalin zaɓen 2027.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet