Featured
Sabon Rikici Ya Yi Sanadiyyar Ƙonewar Gidaje Biyu A Adamawa
Wani sabon rikici ya barkewa a jihar Adamawa, bayan samu wasu hare-hare a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke cikin kananan hukumomin Lamurde da Guyuk na jihar.
Wannan rikici wanda ya zama kamar al’ada a kowanne lokaci na noman damina a iyakar kananan hukumomin biyu, ya yi sanadin konewar dukiyoyi a ranar Laraba 02 ga Yuli, 2025.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis 03 ga Yuli 2025, inda ta bayyana lamarin a matsayin wani shiryayyen al’amari.
A cewar mai magana da yawun rundunar, Suleiman Nguroje, ya ce wasu da ba a san ko suwaye ba, sun bankawa wasu bukkoki wuta a kauyen Lafiya (Lamurde LGA) da Boshikiri (Guyuk LGA). Wanda yayi sanadiyar konewar Dukiyoyin Mrs. Ododumga Kenneth da Mr. Nura Haruna.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dankombo Morris, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, tare da hanzarta tura jami’ai zuwa yankunan da abin ya shafa, domin hana rikicin ci gaba da kuma kama wadanda ke da hannu a lamarin.
Kwamishinan ya gargadi jama’a da su nisanci tayar da hankali ko aikata duk wani laifi, yana mai cewa doka za ta yi aiki a kan duk wanda aka kama da laifi.
Rundunar ta kuma bukaci al’ummar yankin da su zauna lafiya, su ba da hadin kai, kazalika su sanar da hukumomi duk wani motsi ko aikin da suka ga suna da shakku a kai, domin gaggauta daukar mataki.
