Connect with us

Featured

Ahmed Musa Ya Sha Alwashin Dawo Da Martabar Kano Pillars

Tauraron Super Eagles kuma sabon Janar Manajan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa, ya kuduri aniyar farfado da kungiyar tare da dawo da martabarta a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Afrika.

Wannan alkawari na Musa yana cikin wata sanarwa da sashen yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar ya fitar a ranar Talata 08 ga Yuli 2025 a Kano.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron da Shugaban kungiyar, Alhaji Ali Umar, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa, inda ya bayyana shirinsa na yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin sauya akalar kungiyar zuwa mafi alheri.

Tsohon dan wasan Leicester City da CSKA Moscow ya bayyana Kano Pillars a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyi a Najeriya, inda ya jaddada cewa dole ne a tunkari matsalolin kungiyar na baya-bayan nan ta hanyar hadin kai da ingantaccen tsari.

“Kano Pillars tamu ce kuma tana daga cikin kungiyoyi mafi nasara a Najeriya, amma a ‘yan shekarun nan, labarinta ya canza,” in ji Musa.

“Ina tabbatar wa kowa cewa da hadin kai da goyon bayan mambobin kwamitin gudanarwa, zan yi duk mai yiwuwa wajen dawo da martabar kungiyar domin ta zama daya daga cikin mafiya nagarta ba kawai a Afrika ba har ma a duniya.”

Ya ce gogewar da ya samu a Turai da kuma kasancewarsa tsohon dan wasan kungiyar zai taimaka masa wajen cusa sabbin dabaru da ciyar da Pillars gaba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya amince da nadin Musa a matsayin manajan kungiyar, a wani bangare na kokarin farfado da Pillars da daidaita ta da ingantattun ka’idojin kasa da kasa.

Kungiyar wacce ta lashe gasar Nigeria Professional Football League har sau hudu, na fatan shiga sabon zamani na ci gaba da daukaka a karkashin jagorancin Ahmed Musa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet