Connect with us

Featured

Shehu Sani Ya Yi Alla-wadai Da Hargitsin Da Magoya Bayan Kano Pillars Su Ka Tayar a Wasansu Da 3SC

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi Allah wadai da tashin hankalin da magoya bayan kungiyar Kano Pillars suka haifar bayan wasan su da Shooting Stars (3SC) a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Lamarin ya faru ne bayan da dan wasan 3SC, Adams Mustapha, ya zura kwallo a minti na 94, wanda ya kawo wasan 1–1, abinda ya tayar da hankalin magoya bayan na Pillars.

Bayan kammala wasa, wasu magoya bayan Kano Pillars sun mamaye fili tare da kai wa alkalai da ’yan wasan Shooting Stars hari. Bidiyo daga kafar Propel Sports ta nuna yadda aka tilasta wa alkalin wasa Mohammed Tuta da tawagarsa su gudu don tsira, yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa taron. Wasu ’yan wasan 3SC, ciki har da Ismail Ayodele da Adams Agba’a, sun sha duka a cikin rudanin.

Shehu Sani ya bayyana a shafinsa na X cewa wannan hali “abin takaici ne, kuma abin Allah wadai ne.” Ya nuna damuwa kan yadda rashin tsaro da yawan ’yan daba a filayen wasa ke hana masu sha’awar gasar cikin gida zuwa kallon wasanni cikin natsuwa. Ya ce yawanci raba hankali ake yi, ana kallon wasa ana kuma tsaron kai da abin hawa.

Har yanzu hukumar NPFL ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan tashin hankali. Masu sha’awar wasan sun bukaci a dauki mataki mai tsauri don kare ’yan wasa da alkalai, tare da tabbatar da tsaro a filayen wasannin kasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet