Featured
Yajin Aikin ASUU: Duk Malamin Da Bai Je Aiki Ba Ba Za a Bashi Albashi Ba – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da ta sake nazarin matsayarta na shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa tattaunawa ce hanya mafi inganci wajen warware matsalolin da ke fuskantar sashen ilimin gaba da sakandare. Ministocin Ilimi Dr. Maruf Tunji Alausa da Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad sun bayyana cewa gwamnati ta gabatar da cikakken tayin da ya shafi bukatun ASUU, ciki har da walwala, yanayin aiki da tsarin mulki a jami’o’i, tana kuma jiran martanin ƙungiyar.
Gwamnati ta ce ta amince da sabon tsarin “Teaching Allowance” domin karfafa gwiwar malamai, tare da yin gyare-gyare a yanayin aikin su. Sai dai wasu bukatun da suka shafi mulkin cikin gida na jami’o’i sun rage karkashin ikon majalisun gudanarwa na kowane jami’a, inda ake ci gaba da aiwatar da su. Duk da wannan yunƙuri, gwamnati ta nuna cewa ASUU ba ta nuna sahihin martani ba, kuma ta dage kan shiga yajin aiki.
Ministocin sun nanata cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na da cikakken niyyar inganta jin daɗin malamai da tabbatar da zaman lafiya a jami’o’i. Sun kuma tunatar da ASUU cewa dokar “No Work, No Pay” tana nan daram a kundin dokokin ƙwadago na ƙasa, kuma gwamnati za ta aiwatar da ita idan ƙungiyar ta ci gaba da yajin aiki.
A ƙarshe, gwamnatin ta tabbatar da cewa tana buɗe ƙofa ga tattaunawa tare da ASUU da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ci gaban jami’o’i, inganta walwalar ma’aikata da kuma kare kalandar karatu daga rugujewa. Ta jaddada cewa makomar ɗalibai da zaman lafiyar tsarin ilimi ya fi muhimmanci fiye da sabani.
