Featured
Maki 150 Ne Mafi Ƙaranci Don Samun Gurbin Shiga Jami’a – JAMB
Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami’o’i ta Najeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar.
Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar da babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Haka kuma hukumar ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbi kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100.
Wannan na nufin cewa hukumar JAMB ba za ta yarda wata jami’a ta karɓi ɗalibi da ya fadi ƙasa da maki 150 ba a jarrabawar UTME ta shekarar 2025.
Sai dai wasu jami’o’i irin su Jami’ar Ibadan, Jami’ar Pan-Atlantic, da Jami’ar Legas sun sa tazara inda suka ɗora iyakar makin shigowa a 200.
