Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙayyade Shekaru 16 A Matsayin Mafi Ƙarancin Shekarun Shiga Jami’a

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙarancin shekarun da ɗalibai za su iya fara karatu a manyan makarantu na gaba da sakandare a ƙasar.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata 08 ga Yuli, 2025 yayin Taron Tsare-tsaren Shiga Makarantu na 2025 da Hukumar JAMB ta shirya a birnin Abuja.

Alausa, yayin da yake bude taron, ya jaddada cewa wannan ƙa’ida ta shekarun shiga makaranta yanzu doka ce kuma ba za a sassauta ta ba. Ya gargadi cewa duk wani shigar da aka yi ba ta hanyar tsarin CAPS (Central Admissions Processing System) ba, za a ɗauke ta a matsayin ba bisa ƙa’ida ba.

Ministan ya kara da cewa duk shugaban makarantar da aka kama da laifin karɓar ɗalibai ta barauniyar hanya ko ƙetare tsarin CAPS, za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka.

Wannan taron na shekara-shekara ana amfani da shi ne wajen tsara dokoki da ka’idoji na karɓar ɗalibai zuwa jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha, da kwalejojin ilimi a kakar karatu mai zuwa.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet