Connect with us

Featured

Da Yiwuwar Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Kudin Wutar Lantarki A Najeriya

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin komawa tsarin biyan kudin wuta da ya dace da farashin mai kyau domin dakile karin bashin Naira tiriliyan 4 da ake bin bangaren na wutar lantarki.

Ministan ya fadi hakan ne yayin taron hadin gwiwa na Mission 300 da aka gudanar a Abuja, inda ya ce wannan mataki yana cikin gyare-gyaren da ake shirin aiwatarwa don ceto bangaren daga tabarbarewa da kuma kawo ci gaba mai dorewa.

Duk da karin kudin wuta da aka yi wa masu amfani da Band A, jama’a na ci gaba da korafi kan karancin isar da wuta da kuma ci gaba da biyan kudin gyaran na’urorin da ba sa aiki yadda ya kamata ba.

Adelabu ya ce wannan mataki yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

“A halin yanzu, akwai dimbin bashi da ake bin Gwamnati daga kamfanonin samar da wuta wanda ya kai kusan Naira tiriliyan 4 tun daga watan Disamba 2024. Gwamnati na kokarin ganin an rage wannan bashi tare da dakatar da ci gaba da tara sabon bashi ta hanyar sauya tsarin zuwa tsarin biyan kudin da ya dace da farashin da ake kashewa wajen samar da wuta.”

Wannan na nufin cewa Gwamnatin Tarayya za ta janye tallafin da take bayarwa, wanda hakan zai haifar da karin kudin wuta ga dukkan bangarori.

Rahotannin Daily Trust sun bayyana cewa a cikin watanni shida na farko na 2025, gwamnatin ta kashe Naira tiriliyan 1.1 a matsayin tallafi, wanda ya haifar da karin bashin da ya kai Naira tiriliyan 5.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin za ta mai da hankali wajen habaka samar da wuta ta hanyar amfani da wasu hanyoyi masu araha da tsafta, domin rage tsada da dogaro da makamashi guda.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet