Featured
Kungiyoyi Biyu Daga Jihar Kano Za Su Buga Gasar Firimiyar Najeriya A Kakar Wasa Ta 2025/2026
Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC dake jihar Kano da kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourists dakai jihar Bauchi, sun samu tikitin shiga gasar Firimiya ta kasa da za’a fafata ta shekarar 2025/2026.
Kungoyoyin sun samu wannan damar ne biyo bayan masarar suka samu a wasannin da suka fafata da safiyar wannan rana ta Alhamis 10 ga Yuli 2025 a filin wasa na Stephen Keshi da ke jihar Delta.
Barau FC dai ta doke kungiyar kwallon kafa ta Doma United ne da ci biyu da nema, yayin da Wikki Tourists ta lallasa Yobe Desert Stars da ci Hudu da nema.
Wannan dai zai kasance karo na farko da za’a samu ƙungiyoyi biyu daga jihar Kano, da zasu fafata a gasar Firimiya Lig ta kasa tun bayan shekaru da dama.
Masana da dama ganin cewa Ankara samun wata hanyar samun kudin shiga musamman a bangaren wasanni a jihar Kano, kazalali wasu na ganin hakan zai haifar da wasan hamayya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars da Kuma takwarar ta ta Barau FC.
