Featured
Da A Najeriya Buhari Ya Yi Jinya Da Tuni Ya Daɗe Da Mutuwa — Femi Adesina
Tsohon Mai Baiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa da ace tsohon shugaban na Najeriya ya dogara kacokan da asibitocin cikin gida wajen kula da lafiyarsa, da bai kawo yanzu ba.
Adesina ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels Television a ranar Talata 15 ga Yuli, a gabanin jana’izar tsohon shugaban kasa da ya rasu a ranar Lahadi.
Da yake mayar da martani kan suka da dama da Buhari ya sha dangane da yawan zirga-zirgar jinya zuwa Birtaniya a lokacin mulkinsa, Adesina ya ce wannan ba al’amari ne na jin daɗi ba, sai dai bukata ce ta rayuwa.
“Tun kafin ya zama shugaban ƙasa Buhari ya saba yin gwaje-gwajen lafiyarsa a London. Don haka ba wai lokacin da yake mulki ne kawai ya fara zuwa can ba. Likitocin da ke kula da shi can tun can ne suke masa magani,” in ji Adesina.
A cewarsa, waɗanda ke duba lafiyar Buhari a London sun riga sun fahimci tarihin lafiyarsa, don haka ba hikima ba ce a dakatar da su a tsaka da jinya domin a nemi sabbin likitoci a cikin gida.
Ya ce shawarar ci gaba da jinya a ƙetare ya ta’allaka ne da ƙwarewa da kuma iyakacin da tsarin kiwon lafiya na Najeriya ke da shi a lokacin.
“Dole mutum ya kasance da rai kafin a gyara wasu abubuwa a ƙasa. Da Buhari ya ce zai dinga yin jinyarsa a gida don nuna ƙaunar ƙasa ko wani dalili makamancin haka, da tuni ya dade da mutuwa — domin watakila babu ƙwarewar da ake buƙata a nan gida,” in ji shi.
Adesina ya ƙara da cewa rayuwar Buhari da ikon da ya samu na shugabantar Najeriya ba zai yiwu ba da ba don kulawar da ya samu daga likitocin ƙetare ba.
Ya bayyana cewa ya kamata a fahimci yawan tafiyarsa jinya a waje a matsayin abin da ya zama dole saboda halin da ake ciki a wancan lokacin, ba wani alamar raini ga asibitocin Najeriya ba ne.
