Connect with us

Featured

Har Yanzu Kwankwaso Bai Yanke Shawarar Shiga Kowace Jam’iyya Ba – Dungurawa

Shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya bayyana cewa jagoran jam’iyyar na kasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, bai yanke wata shawara ta shiga hadaka da wata jam’iyya ko sauya sheka zuwa wata sabuwar jam’iyya ba, sabanin rade-radin da ke yawo a wasu sassa na kasar.

Dungurawa ya bayyana hakan ne a jiya litinin 14 ga Yuli, yayin wata hira da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya ce Kwankwaso ba dan siyasa ba ne da ke yanke shawara cikin gaggawa ko rashin tsari.

A cewar sa “Dukkan rade-radin da ake yi na cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ko wata daban, karya ce kawai da wasu ‘yan siyasa ke yadawa saboda tsoron tasirin da yake da shi a siyasar kasar nan, musamman a Arewacin Najeriya.”

Dangane da kokarin wasu da ke danganta Kwankwaso da wasu jam’iyyu, Dungurawa ya ce: “A halin yanzu, babu wani lokaci da ya dace da yanke irin wannan shawara. Ya kamata ‘yan siyasa su nutsu su bar surutai marasa tushe. Kwankwaso mutum ne da ke daukar mataki bisa cikakken tunani da shawara.”

Dungurawa ya kammala da cewa “Wasu magoya bayan Kwankwaso da ke nuna damuwa a kan inda ya dosa, ba masu gaskiya ba ne. Wadanda suka san Kwankwaso da gaske, sun san cewa ba ya daukar matsaya sai da ya tuntubi magoya bayansa tun daga matakin mazaba har zuwa sama.”

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet