Connect with us

Featured

Jami’an ‘Yan Sanda 151 Na Fuskantar Barazanar Kora Ko Rage Matsayi Sakamakon Karya Dokokin Aiki

Akalla jami’an ‘yan sanda 151 da suka hada da manyan jami’ai daga sassa daban-daban na Najeriya na fuskantar kwamitin ladabtarwa da aka kafa a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa bisa zargin aikata laifukan da suka hada da keta ka’idojin aikin dan sanda, rashin da’a da kuma cin amanar aiki.

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa akwai yiyuwar wasu daga cikin jami’an za su fuskanci kora daga aiki yayin da wasu kuma za a rage musu matsayi, duba da yadda binciken ke tafiya. Wannan na zuwa ne bayan Rundunar ta sallami jami’ai 34 tun bayan zuwan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, a shekarar 2023.

Kwamitin ladabtarwar, wanda ya fara zama tun ranar Litinin 14 ga Yuli a Abuja, zai dauki kwanaki goma kafin ya mika rahotonsa ga Hukumar Ayyuka ta ‘Yan Sanda wadda ke da ikon daukar matakin ladabtarwa.

Binciken na faruwa ne a daidai lokacin da rundunar ke karɓar kararraki daga lauyoyi, kungiyoyin farar hula da ‘yan kasuwa dangane da zarge-zargen cin zarafi, karɓar rashawa, da hannu cikin sace mutane.

A baya, hukumar ayyuka ta ‘yan sanda ta yi amfani da matakai irin su kora, rage girma ko gurfanar da masu laifi a gaban kotu don zama izina ga sauran jami’ai.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana zargin wasu daga cikin jami’an da hannu a yunkurin shirya zanga-zanga kan matsin tattalin arziki da rashin kulawa da walwalarsu.

Wata majiya ta ce, “Ba a taba samun yawan jami’ai da yawa da ke fuskantar hukunci a lokaci guda irin haka ba”.

Wani ya kara da cewa an danganta wasu daga cikin jami’an da zuga tsofaffin jami’ai su rika sukar shugabancin yan sanda na yanzu, saboda batun tsarin fansho da bai yi musu dadi ba.

Mai magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin da’a ba. Ya ce kwamitin ladabtarwa yana bin tsarin doka da ka’ida domin tabbatar da adalci.

Ya kara da cewa, “Sufeto Janar ya jaddada kudurinsa na tabbatar da da’a da gaskiya a cikin rundunar. Za a hukunta duk jami’in da aka samu da laifi bisa bin doka da oda.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet