Connect with us

Featured

Najeriya Ba Ta Yi Niyyar Magance Matsalar Wutar Lantarki Ba — Aliko Dangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce babu wani dalili da zai sa Najeriya ta ci gaba da fama da ƙarancin wutar lantarki, yana mai cewa idan har kamfaninsa kaɗai na iya samar da sama da megawatt 1,500 don amfani na cikin gida, to ya kamata a ce ƙasar ta fi haka nesa ba kusa ba.

Dangote ya bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai wa matatar man Dangote da ke Lagos, inda ya jaddada yadda kamfaninsa ke faɗaɗa harkokin samar da makamashi.

A cewarsa, bai kamata Najeriya ta ci gaba da jan ƙafa a tsakanin megawatt 4,500 zuwa 5,000 ba, sai dai kamata ya yi a rika samar da megawatt 60,000.

Ya ce, “Mu dai kamfaninmu kaɗai muna samar da sama da megawatt 1,500 don amfanin kanmu. Don haka, Najeriya bai kamata tana samar da ƙasa da sau uku na abin da muke samarwa ba. Ya kamata tana da megawatt 50,000 zuwa 60,000.”

Dangote ya ce abinda suka cimma a wajen gina matatar man ya nuna cewa manyan ayyuka na masana’antu suna yiwuwa a Najeriya, har da na fannin samar da wuta.

Ya ƙara da cewa, “Abinda muka yi a nan matatar man ya nuna babu abinda ba zai yiwu ba. Duk wannan yana iya faruwa a fannin wutar lantarki. Babu dalilin da zai sa Najeriya ta tsaya a megawatt 5,000.”

Attajirin ya ce gina matatar man ya fi wahala fiye da samar da megawatt 30,000 na wuta a Najeriya, kuma gina wannan tsarin bai kamata a ɗora shi kacokan kan gwamnati ba.

A cewarsa, “Abinda muka aikata a nan ya fi wahala fiye da samar da megawatt 25,000 ko 30,000 da tsarin tura da rarraba wuta. Amma wannan ba aikin gwamnati kaɗai bane.”

Ya tunatar da cewa an riga an keɓe fannin wutar lantarki, yana mai kira ga ‘yan Najeriya masu kuɗi da su daina fitar da jari zuwa ƙasashen waje, su zuba su a cikin gida don bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Ya ce, “Mun riga mun buƙaci gwamnati ta fice daga fannin. An riga an keɓe shi. Ya kamata mu ‘yan kasuwa, musamman mu ‘yan Najeriya, mu daina fitar da kuɗinmu zuwa waje, mu zuba su a nan cikin ƙasa domin mu bunƙasa ƙasarmu da nahiyarmu.”

Dangote ya danganta fitar da jari zuwa kasashen waje da koma-baya a ci gaban ƙasa, yana caccakar masu sace kuɗin al’umma da ɓoyewa a ƙasashen waje maimakon zuba su a gida.

Ya ce, “Ina faɗi a kai a kai: babu wata ƙasa da ba ta da rashawa. Wasu ƙasashe ma sun fi mu rashawa, amma suna bunƙasa. Babban matsalarmu shine: waɗanda suka sace kuɗi suna fita da su zuwa waje.

“Don haka waɗancan kuɗaɗen ba su amfanar da su, ba su amfanar da iyalansu, domin ba za su iya nuna wa iyalansu ba cewa kuɗin sata ne. Sannan kuma ba su zuba su a gida ba domin haɓaka tattalin arziki.”

A ƙarshe, Dangote ya ce cikin watanni 40 masu zuwa, yana shirin zama babban mai samar da takin zamani mafi girma a duniya, inda zai faɗaɗa samar da takin zuwa ton miliyan 12 a shekara.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet