Connect with us

Featured

Bayelsa Ta Buƙaci A Ƙirƙiro Ƙarin Ƙananan Hukumomi 25 A Jihar

Bayelsa ta nemi a ƙirƙiri ƙananan hukumomi guda 25 a jihar, domin ƙara adadin ƙananan hukumomin da ke jihar daga takwas zuwa 33.

Wannan bukata ta fito ne daga bakin Atoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Mista Biriyai Dambo (SAN), a lokacin wani taron jin ra’ayin jama’a da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya shirya a ranar Asabar 19 ga Yuli, a Dakin Taro na DSP Alamieyeseigha da ke Yenagoa.

Taron ya haɗa da masu ruwa da tsaki daga jihohin Bayelsa, Delta da Edo, kuma yana daga cikin shirin nazari da gyaran tsarin mulkin ƙasa da ke gudana a sashen Kudu maso Kudu (South-South Centre A).

Dambo ya bayyana cewa buƙatar ƙarin ƙananan hukumomin na da muhimmanci domin yawan unguwannin da ke cikin wasu kananan hukumomin sun zarce kima, lamarin da ke sanya ayyuka su wuce ƙarfin gwamnati.

Ya kuma ce jihar na da tsari da ƙarfin tattalin arziki da za ta iya ɗaukar nauyin sabbin ƙananan hukumomin da ake so a ƙirƙira.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Gwamnan Bayelsa, Daniel Alabrah, ya fitar, an bayyana cewa jihar ta gabatar da wasu buƙatu da dama da suka haɗa da:

Sauya tsarin ƙananan hukumomi da ba su ‘yancin cin gashin kansu,

Gyara jerin dokokin da ke cikin “exclusive” da “concurrent list”,

Gyaran tsarin zaɓe domin tabbatar da sahihancin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC),

Da kuma gyaran shari’a domin tabbatar da adalci cikin sauƙi da sauri.

Jihar ta kuma nemi a sake fasalin tsarin tarayya (federalism) na ƙasar, domin a ba jihohi cikakken iko kan albarkatun da ke ƙasarsu ko a cikin ruwa (onshore da offshore), sannan su riƙe kashi 60% na kuɗin shiga da suka samar, su miƙa 40% zuwa Gwamnatin Tarayya.

Dangane da tsaro, Bayelsa ta goyi bayan samar da ‘yan sandan jihohi (state police), inda ta ce lokaci ya yi da za a rungumi tsarin ‘yan sanda masu cin gashin kansu domin ƙarfafa tsaron cikin gida.

Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana gyaran tsarin mulki da ake yi a matsayin matakin da ya dace da lokacin, domin daidaita dokokin ƙasa da halin da ake ciki a yanzu da kuma buƙatun jama’a.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet