Connect with us

Featured

Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Yahaya Bello Domin Tafiya Turai Neman Magani

A Litinin din nan 21 ga Yuli, 2025. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, inda ya nemi a bashi fasfo ɗinsa domin ya tafi ƙasashen waje neman magani.

Kotun ta yi watsi da buƙatar ne saboda rahoton lafiyar da aka haɗa da buƙatar bai da sa hannun likitan da ya rubuta shi.

Bello, wanda ke fuskantar tuhumar almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati har Naira biliyan 80.2, a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite, wadda hukumar EFCC ta shigar, ya nemi a dawo masa da takardun tafiyarsa domin neman magani a Birtaniya.

Har ila yau, Bello yana fuskantar shari’a makamanciyar wannan a gaban Mai Shari’a Maryanne Anenih a Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama.

A kotun FCT ma Bello ya shigar da buƙatar makamanciyar wadda ya shigar a kotun tarayya, amma mai shari’ar ta bayyana cewa fasfo ɗin ba ya hannun kotunta, domin tuni an mika shi ga Babbar Kotun Tarayya.

Ta ce ko da kotun ta amince da buƙatar, hakan ba zai yi tasiri ba tunda takardar tafiyar ba ta hannunta ba ce.

Tuni dai EFCC ta nuna adawa da buƙatar, inda ta ce shigar da irin wannan buƙata a kotu biyu lokaci guda abu ne da zai iya haifar da sabanin hukunci da kuma tauye martabar shari’a.

Sai dai a hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya ce, akasin hujjar EFCC, wannan buƙata ba ta zama cin zarafin tsarin kotu ba.

Lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu (SAN), ya gabatar da hujjoji ciki har da takardu guda biyu — “Exhibit A” da “Exhibit B” — da ke bayyana cewa dan uwansu yana fama da hawan jini tun sama da shekara 15.

Amma kotu ta ce Exhibit B — rahoton lafiyar da aka gabatar — bai da sa hannu, don haka bai da wata daraja a doka.

“Takarda da ba a sa hannu ba bata da wani amfani a doka. Wannan rahoto bai da wani ƙima da zai sa kotu ta dogara da shi,” in ji mai shari’a.

Dangane da batun masu tsayawa masa a kotu (sureties), kotun ta yanke hukunci cewa wannan ƙara tsakanin Yahaya Bello da Gwamnatin Tarayya ce, ba wai tsakanin sureties ba.

Mai shari’a Nwite ya ƙara da cewa: “Lauyan wanda ke ƙara bai kawo wata doka da ke cewa dole ne a sanar da masu tsaya masa kafin shigar da wannan buƙata ba.”

A ƙarshe, kotun ta ce rashin sa hannu a rahoton lafiya ya sa ba za ta iya karɓar hujjojin da aka gabatar ba, don haka ba a gamsu da dalilin buƙatar tafiya waje ba.

Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar, kuma ta dage cigaban shari’a zuwa 7, 10 ga Oktoba da 10 da 11 ga Nuwamba, 2025.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet