Featured
Ina So In Amsa Gayyatar Kotu Amma Ina Tsoron Kar A Kama Ni – Yahaya Bello
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a shirye yake ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin amsa tuhume-tuhume 19 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke yi masa.
Yahaya Bello ya bayyana hakan ne ta bakin lauyoyinsa da suka wakilce shi a zaman kotun da aka yi a ranar Talata.
EFCC ta sake maka Emefiele a kotu kan wasu sabbin tuhume-tuhume
Mista Adeola Adedipe SAN, guda cikin lauyoyinsa ya shaida wa kotun cewa, wanda yake karewa yana son gabatar da kansa a gaban kotu amma yana tsoron umurnin da aka bayar na cafke shi.
Don haka, ya bukaci kotun da ta yi watsi da umarnin kama tsohon gwamnan da ta bayar a baya.
