Featured
EFCC Na Neman Abdulrashid Maina Ruwa-a-jallo
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), ta ayyana tsohon shugaban runduna ta musamman, domin sake fasalin tsarin fansho, Abdulrashid Maina a matsayin wanda take nema.
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu ranar Laraba. An gurfanar da Maina da ɗansa Faisal tun a 2019, kan tuhume-tuhumen da suka shafi halatta kuɗaɗen haram, da ɓoye abin da aka samu ta hanyar aikata laifi.
Read Also: NAWOJ Congratulates Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya PhD
Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifimamwancan lokaci, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru takwas a watan Nuwamban 2022.
A sanarwar da EFCC ta fitar, ta ce Maina mai shekaru 61, ɗan asalin Biu ne a Jihar Borno, kuma tana neman duk wanda ke da bayanin inda yake da ya tuntubi ofisoshinta ko ofishin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
