Featured
EFCC Ta Kwato Naira Tiriliyan 1.23 da Dala Miliyan 684 Cikin Watanni 32
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta ce ta kwato Naira tiriliyan 1.23, dala miliyan 684.48, fam 373,905.78 da kuma Yuro miliyan 9.34 tsakanin ranar 1 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yunin 2026.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin 32 ga Agusta, 2026, yayin ganawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida a Abuja, inda ya ce kwato kadarori na daga cikin manyan ginshiƙan ayyukan hukumar.
A cewarsa, kuɗaɗen da aka kwato sun haɗa da kadarori da kuɗaɗen da aka gano suna da alaƙa da laifukan kuɗi, yayin da aka kwato wani kaso mai tsoka daga ciki a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Read Also : Bebeji : Ƴanbindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC na mazabar Rantan
Olukoyede ya ce daga cikin sama da Naira tiriliyan 1.23 da aka kwato, Naira biliyan 397.26, kwatankwacin kashi 33 cikin 100, an kwato su kai tsaye domin gwamnatin tarayya.
Ya ƙara da cewa sauran Naira biliyan 836.34, kwatankwacin kashi 67 cikin 100, an kwato su ne a madadin ma’aikatu daban-daban, yana mai cewa kwato kadarori na ci gaba da zama muhimmin ɓangare na yaƙin EFCC da laifukan tattalin arziki da na kuɗi tare da kare dukiyar jama’a.
